An kashe sama da mutane goma a Gombe

An kai hari a Gombe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai hari a Gombe

Hukumomin tsaro a jihar Gombe ta Nijeriya na cewa mutane goma sha biyu ne suka rasa rayukansu a jerin hare-haren bama-bamai da kuma bindigogi da aka kai jiya da dare a Gombe babban birnin jihar, kodayake dai shaidu na cewa adadin y fi haka.

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce ta kai wasu mutanen da aka raunata zuwa asibiti yayin da dokar hana fita ba dare ba rana ke ci gaba da aiki a birnin, bayan harin na jiya da aka kai kan ofisoshin yan sanda da kuma musayar wuta a babban gidan Yari dake birnin.

Bayanai dai na cewa hukumomi sun tsaurara tsaro a jihar, bayan faruwar lamarin wanda shi ne na baya-bayanan a jerin hare-haren bama-bamai da na bindigar da Nijeriya ke fama dasu musamman a arewacin kasar.

Karin bayani