Nelson Mandela na fama da ciwon ciki

Nelson Mandela Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nelson Mandela

An kwantar da tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela a asibiti.

Wakiliyar BBC ta ce tsohon shugaban na Afrika ta Kudu mai shekaru 93, ya yi jinya ne a asibiti saboda ya jima yana kokawa da wani ciwon ciki, wata guda bayan ya bar gidansa dake Eastern Cape zuwa birnmin Johanesburg.

Wasu majiyoyi a Afruka ta Kudun sun shaidawa BBC cewa Mr Mandela yana magana, tare da sanmun sauki bayan tiyatar da aka yi mashi, kuma mai yiwa a sallame shi a gobe Lahadi.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake kwantar da Mr Mandela a asibiti a cikin sama da shekara guda da ta wuce.

Ya sauka daga karagar mulki ne shekaru 8 da suka wuce.

Karin bayani