Najeriya ta kori wasu 'yan kasashen Nijar da Chadi

Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Najeriya ta hada iyaka da kasashen Nijar da Chadi

Hukumar shige da ficen Najeriya ta ce ta mayar da kimanin mutane dubu goma sha daya 'yan Nijar da Chadi kasashen su na haihuwa saboda rashin cikakkun takardun zama a kasar.

Kakakin hukumar ya shaida wa BBC cewa an mayar da mutanen ne bisa rashin cikkakun takardun zama a Najeriya.

Sai dai hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro, musamman daga kungiyar nan ta jama'atul Ahlul sunna lil da'a wati wal jihad ko kuma Boko Haram.

"Kawo yanzu hukumar ta kwashe 'yan kasashen Nijar da Chadi da Mali da jamhuriyar Benin 11, 000 zuwa kasashensu. Acewarsa hukumar ta yi hakan ne saboda basu da cikakkun takardun zama a kasar," a cewar kakakin hukumar Mr. Joachim Olumba.

Mr. Olumba ya kuma kara da cewa ana kwashe wadannan mutane ne don maida su kasashensu daga sassa daban- daban na kasar, inda ko a makon da ya gabata ma an kwashe mu 91 daga Abuja, sannan kuma an maida wasu mutane 'yan wadannan kasashe su 30 gida daga jihar Ogun.

Sai dai kakakin hukumar ta shige da ficen ya bayyana cewa ba wai saboda suna zarginsu da alaka da kungiyar Boko Haram ba ne yasa hukumar ta maida su gida ba, illa kawai kan dalilin rashin cikakkun takardun zama.

Sai dai shugabar ofishin jakadancin Nijar a arewacin Najeriya, Rabi Abdu ta shaida wa BBC cewa bata da cikakken bayanin abinda ke faruwa saboda haka ba za ta iya cewa komai a yanzu.

Hakan dai na zuwa ne adaidai lokacin da bakin iyakar Najeriyar ta kananan hukumomin dake fuskantar dokar ta baci ke ci gaba da kasancewa a rufe, yayinda kuma kungiyar Boko haram ke ci gaba da kai hare-hare.

Karin bayani