Kungiyar FARC a Colombia ta fara sassauci

Kungiyar 'yan tawayen Farc Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar 'yan tawayen Farc

Kungiyar 'yan tawaye mafi girma a Colombia ta FARC, ta ce za ta saki dukannin mutanen da take garkuwa da su, ta kuma daina sace mutane.

Ana kyautata zaton 'yan tawayen masu ra'ayin sauyi, suna rike da akalla jami'an tsaron Colombian su 10 da kuma fararen hula da dama.

Wannan mataki dai ya zo ne watanni 3, bayan da kungiyar ta FARC ta kashe mutane 4 da ta shafe shekaru fiye da 12 tana garkuwa da su, abun da ya haddasa jerin zanga-zangar nuna kin jininsu a duk fadin kasar ta Colombia.

'Yan tawayen na FARC dai suna gwagwarmaya ne domin hambarar da gwamnatin Colombia tun shekarun 1960, kuma suna amfani da fataucin miyagun kwayoyi da kuma garkuwa da mutane, wajen samun kudaden shiga.

Karin bayani