Shugaba Goodluck ya yi Allah wadai da harin Jos

An kai hari wani coci a Jos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kai hari wani coci a Jos

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a kan wani Coci a birnin Jos na jihar Pilato dake tsakiyar Najeria, ya janyo hare-haren ramuwar gayya daga bangaren wasu Kiristoci da suka fusata.

Mutane uku ne dai suka rasa rayikansu, wasu karin 40 kuma suka jikatta a lokacin da wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse a cikin harabar ginin majami'ar COCIN dake Jos din.

Wakilin BBC ya ce daga bisani sai wani gungun matasa Kiristoci suka kai ware hare-hare da suka yi kama da na ramuwar gayya inda wasu 'yan jarida dake wurin suka ce an kashe akalla Musulmi 2, tare da kokkona wasu shaguna.

Kungiyar nan ta masu kishin Islama da aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ta kai harin a kan majami'ar ta COCIN.

Karin bayani