Nelson Mandela ya samu sauki

Nelson Mandela Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nelson Mandela

An sallami tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela daga asibiti, kwana daya bayan da aka kwantad da shi saboda wani ciwon ciki da ya jima yana kokawa da shi.

Likitoci sun yanke shawarar sallamar shi ne saboda gwaje-gwajen da suka gudanar akan shi sun nuna cewa babu wani abun nuna damuwa sosai game da lafiyarsa.

An dai yiwa Mr Mandelan tiyata ne inda aka saka ma shi wata 'yar camera cikin cikinsa.

Wani ministan Afirka ta Kudu ya ce Mr Mandela ya samu sauki.

Karin bayani