Ana rusa gidan Osama bin Laden

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Osama Bin Laden

Rundunonin tsaron Pakistan suna ci gaba da aikin rusa gidan da dakarun Amurka suka kashe Osama bin Laden a watan Mayun da ya gabata.

Tuni dai manyan katafilu, wadanda suka isa wurin da almurun ranar Asabar, suka share wani sashe mai girma na gidan.

An kuma tsaurara matakan tsaro sosai a kewayen gidan, inda jagoran na kungiyar Al-Qaida ya kwashe fiye da shekaru biyar yana boye.

Hukumomin Pakistan din suna so ne su hana gidan zama wurin ziyara.

Karin bayani