Ana kuri'ar raba-gardama a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zangar adawa da kuri'ar raba-gardama a Syria

A kasar Syria, gwamnati ta yi kira ga 'yan kasar da su fito don kada kuri'a a kuri'ar raba-gardama, don samar da sabon kundin tsarin mulki, wanda ake gudanarwa yau Lahadi, duk da rikicin da ke kara ruruwa.

Wannan kuri'a ce dai kashin bayan sauye-sauyen da Shugaba Bashar al-Assad ya yi tayin aiwatarwa tun lokacin da aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa kusan shekara guda da ta gabata.

Sabon tsarin mulkin dai zai samar da tsarin jam'iyyu masu yawa a kasar ta Syria, sai dai kuma kungiyoyin 'yan adawa sun yi kira da a kauracewa kuri'ar raba-gardamar.

Daya daga cikin kungiyoyin 'yan adawar ta bayyana zaben da cewa wata yaudara ce kawai.

Ta ce gwamnatin shugaba Assad ba ta taba mutunta ko da kundin tsarin mulkin kasar na yanzu ba, wanda ya baiwa 'yan kasar 'yancin fadin albarkacin bakinsu, da na gudanar da zanga-zangar lumana, kana ya hana cin zarafin jama'a.

An dai zuba ido a ga yadda za a gudanar da wannan kuri'ar raba-gardama a irin yanayin tashin hankalin da kasar ke ciki.

Karin bayani