'Yan Syria na neman sauyin siyasa

Image caption Zaben raba gardama

Shugaban Syria Bashar al Assad ya kada kuria a zaben rabagardama kan wani sabon tsarin mulkin kasar, wanda ya ce zai maida Syriar wata kasa da zaa yi koyi da ita a fannin Demokradiyya.

An tsawaita lokacin kada kuria a wasu yankuna na birnin Damascus.

Wakilin BBC ya ce gidan talabijin na kasar ta Syria ya nuna jamaa na kada kuria a Damascus da sauran wurare cikin lumana, amma a wasu wuraren ba haka, batun yake ba.

Sai dai kungiyoyin adawa sun yi watsi da kuriar, suna masu cewa wata yaudara ce.

Sun ce mutane akalla 30 ne aka kashe a yinin yau, kuma galibinsu an hallka su ne a birnin Homs inda sojojin gwamnati ke cigaba da luguden bama-bamai.

Kungiyar agaji ta Red Cross ko Croix Rouge, ta ce har yanzu hukumomin Syriar ba su amsa bukatar da ta gabatar ma su ba, ta a tsagaita wuta a kowacce rana, domin kungiyar ta samu damar kwashe mutanen da suka ji raunika daga birnin

Karin bayani