Dan jarida mai rauni daya aka tabbatar da fitarwa daga Syria

Edith Bouvier Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Edith Bouvier

Har yanzu akwai rashin tabbas game da yar Jaridar Faransan nan da ta samu rauni, Edith Bouvier.

A halin yanzu Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya yi amai ya lashe dangane da kalamin cewar ita ma an fice da ita a sace zuwa Lebanon.

Jaridar da take wa aiki, Le Figoro, ta ce har yanzu tana a cikin Syria.

Tun farko dai masu fafutika na Syria sun taimaka ga satar fita da wani mai daukar hoto dan Birtaniya, Paul Conroy, wanda ya makale a Homs tun lokacin da aka jikkata shi makon da ya wuce.

An dai bayar da rahoton cewa masu fafutika da yawa ne aka kashe a wani kokari na fitar da shi daga unguwar Baba Amr da aka yi wa luguden wuta.

Karin bayani