Masu sauraron BBC sun karu a Iran

Image caption Tambarin BBC

Yawan masu kallo da sauraron tashohin labarai na BBC a Iran ya karu da kashi tamanin da biyar cikin dari duk kuwa da abin da kafar yada labaran ta kira yawan tace shirye-shiryenta da kuma kurari daga hukumomi.

Wani bincike mai zaman kansa ya nuna cewa a yanzu mutane kusan miliyan shida ne ke kallon tashar talabijin ta BBC mai watsa shirye-shiryenta da harshen Farsi duk mako.

Wadannan alkaluma sun dace da lokacin da Sashen BBC mai watsa shirye-shiryensa ga kasashen waje ke cika shekaru tamanin da kafuwa.

A yinin ranar Talata dai za a gabatar da shirye-shirye na musamman, wadanda suka hada da na harshen Ingilishi da na sauran harsuna a Bush House da ke Landan.

Karin bayani