Amurka za ta tallafawa Koriya ta Arewa

Sakatariyar wajen Amurka, Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakatariyar wajen Amurka, Hillary Clinton

Koriya ta arewa ta bada sanarwar dakatar da shirin inganta makamashin nukiliyarta tare da dakatar da gwaje-gwajan makamai masu linzami dake da nisan zango, biyowa bayan tattaunawarta da Amurka.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta ce har ila yau Koriya ta arewa ta aminca ta bar Majilar Dinkin Duniya ta tabbatar cewa ta aiwatar da hakan.

Da take magana Washington, Mrs Clinton ta ce Koriya ta arewa ta yi abinda ta kira daukar matakin da ya dace.

Ana ta bangaran kuma Amurka za ta yanke shawara kan tallafin abincin da zata ba Koriya ta arewan da yawansa ya kai tan dubu dari biyu da arba'in.

Karin bayani