An kori Bo Xilai daga Ofishinsa a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hoton Bo Xilai

An kori daya daga cikin manyan Jami'an Kasar China daga ofishinsa, bayan wata badakala da ta girgiza Kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasar Shinhua, yace an maye gurbin Bo Xilai, a matsayin Shugaban Jam'iyya a Chongqing, daya daga cikin manyan biranen Chinan.

Bo Xilai na daya daga cikin yan kwalisar yan siyasa a china. Ya jima da kasancewa mutumi dan takara ga babban mukamin shugabanci a Kasar.

Amma badakala ta kunno kai watan da ya gabata bayanda wani tsohon babban jamiin tsaronsa ya kwana a karamin ofishin jakadancin Amurka. Inda akayi zargin dansadan da neman ya samu mafaka.

Tun dai wannan lokacin ne ake ta yada jita jita akan makomar Bo Xilai nan gaba.

Yanzu kuma da aka tunbukeshi daga mukamin nasa, za aita batutuwa ne akan samun sauyin shugabancin Jamiyyar a China nan gaba a wannan shekarar.

Da, ana saran dai Mr Bo, zai shiga wani kwamitin Politburo mai mambobi tara da yake gudanarda harkokin Kasar ta China.

Karin bayani