An tafi da Sojan Amurka zuwa Kuwaiti

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Afghanistan

Jami'in Kungiyar North Atlantic Treaty Organization, wato NATO ya tabbatarwa da BBC cewa sojan nan na Amurka wanda aka zarge shi da alhakkin harbin yan Afghanistan an futardashi zuwa Kuwait.

Sojan dai wanda ake zargin ya kashe mutane goma sha shida ciki harda kananan yara tara yan afghanistan a karshen mako

Wannan ya nuna cewa akwai dai kyakkyawar fahimta daga bangaren gwamnatin Afghanistan da ta bari aka dauke sojan da ake magana akansa zuwa wajen kasar.

Amma hakan ba zai tsinana komai ba wajan rage kaifin fushin da yan Kasar Afghanistan da dama suka furta , wanda suka bukaci a gurfanardashi a gaban kuliya a Afghanistan din.

Ko da yake nukatar tasu dama ba zata samu ba, tunda Amurka ta futo karara cewa ko wane sojanta da aka zarge shi da aikata wani laifi zaa hukuntashi ne a karkashin tsarin dokokin sojin kasarta Amurka.

Sojan dai da aka zarga da kisa a Kandahar ba a zayyana sunansa ba har yanzu wanda hakan tsari ne na sashin tsaro na Amurka har sai an futo da tuhume tuhumen da ake masa.

Sai dai an rawaito Hukumomin tsaron Amurka na cewa wanda ake zargin na da tarihin gushewar hankali da kuma damuwa ta iyali kafin a turoshi Afghanistan din.

Karin bayani