Za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban Kasa a Senegal

Shugaba Wade na Senegal Hakkin mallakar hoto
Image caption Za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban Kasa a Senegal

Hukumomin zabe a Kasar Senegal sun ce za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban Kasa, bayan Shugaban Kasar mai ci yanzu Abdullahi Wade ya gaza samun rinjayen kuri'u a zagayen farko na zaben.

Mr. Wade dai ya samu kashi 35 cikin 100 na kuri'un ne a zaben da aka yi ranar asabar.

A wata mai zuwa ne kuma zai fuskanci abokin hamayyar sa, kuma tsohon Firayim Ministan sa Macky Sall wanda ya zo na biyu da kimanin kashi 26 bisa 100 na kuri'un da aka kada a zaben.

Al'ummar Kasar dai na da bambancin ra'ayi inda wasu ke neman a samu canjin Shugabanci a Kasar