Ban Ki Moon ya soki mahukuntan Syria

Mr. Ban Ki Moon
Image caption Muhukuntan Syria sun aikata miyagun laifuka a kan jama'ar su in ji Mr. Ban Ki Moon

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya fada wa babban zauren Majalisar a birnin New York cewar ba tare da wata tantama ba, muhukuntan Syria sun aikata miyagun laifuka a kan jama'ar su.

Mr. Ban yace ya damu da irin yadda sojojin gwamnatin Syriar ke kisan mutane siddan ragadan, tare kuma da tsare mutane haka kurum tare da gana masu azaba a lardin Baba Amr dake birnin Homs.

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Kasashen duniya su hada kai wajen kawo karshen abinda ke faruwa a Kasar ta Syria.

Jakadan Syriar a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja'afari ya bayyana cewar kalaman na Ban Ki Moon sun biyo bayan ra'ayoyi ne da jita-jita da ake yadawa.

Karin bayani