Sakamakon zaben Wukan a China

Wani mai kada kuria a Wukan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai kada kuria a Wukan

A kudancin China an zabi wasu mutane biyu domin su shugabanci wani kauye inda suka jagoranci boren nuna adawa da yadda jami'an gwamnati ke kwace filaye.

Dubban mutane a kauyen na Wukan ne suka zabi Lin Zuluan da Yang Semao a matsayin shugaba da kuma mataimaki:

Wakiliyar BBC ta ce a watan Disambar bara ne magajin garin dake kula da kauyen Wukan ya bayyana Lin Zuluan da kuma Yang Semao a matsayin masu yada jita-jita.

A watan Disambar baran ne dai mutanen kauyen Wukan suka kori wasu jami'an gwamnatin da suka ce, suna kwace musu filaye.