Kowanne bangare ya keta Hakkin BilAdama a yakin Libya

Wani dan tawaye a lokacin yakin Libya
Image caption Wani dan tawaye a lokacin yakin Libya

Wani rahoton majalisar dinkin duniya da ya duba batun take hakkin bil'adama a Libya ya ce, kowanne bangare ya wuce gona da iri yayin boren da ya kai ga kisan tsohon shugaba, Kanar Mu'ammar Gaddafi.

Kwamitin dake kula da hakkin bil'adama ya ce, dakarun da suka goyi bayan Kanar Gaddafi sun aikata kisa da dama, da azabtarwa, da kuma fyade:

Wakilin BBC ya ce masu binciken sun ce, kokarinsu na binciko yadda aka kashe Kanar Gaddafi ya ci tura saboda hukumomi ba su ba su rahoto ba akan yadda rai ya fita daga jikin Kanar Gaddafin.

Rahoton ya kuma zargi 'yan tawayen Libya da aikata irin laifukan da magoya bayan Kanar Gaddafi suka aikata.

Karin bayani