Mummunan hadarin mota a Guinea ya hallaka mutane 50

Kasar Guinea Hakkin mallakar hoto d
Image caption Mutane 50 sun mutu a wani hadarin mota a Guinea

Rahotanni daga Kasar Guinea sun ce mutane hamsin su ka mutu, akwai kuma a kalla wasu ashirin da suka jikkata a wani hadarin mota.

Wata sanarwa da gwamnatin Kasar ta bayar, ta ce wata motar kiya-kiya ce makare da fasinja dake kan hanyar su ta zuwa kasuwa ta yi hadarin.

Wani mutum da ya shaida lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar, motar ta fada wani kwari ne bayan burkin ta ya shanye lokacin da take kokarin haye wani tudu.

An kwashi mutanen da suka jikkata a hadarin zuwa asibitin Beyla dake kudu maso gabashin Kasar ta Guniea.