Putin ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasa a Rasha

Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Vladimir Putin

Pira ministan Rasha Vladimir Putin ya yi ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasar da aka yi ranar Lahadi.

Mr Putin dai ya yi ikirarin ne a lokacin da ya ke yiwa dubban magoya bayansa wani jawabi mai sosa rai a gaban fadar Kremlin yayinda suke ta shagulgulan murnar wannan nasara da ya samu.

Sakamakon farko na zaben dai ya nuna cewa Mr Putin din ya samu kashi 60 daga cikin 100 na kuru'un da aka kada, amma har yanzu ana cigaba da kidayar kuru'u.

Sai dai 'yan adawa sun zargi gwamnati da tafka magudi a zaben a wurare.

Wakilin BBC ya ce a gobe ne 'yan adawan za su yi gangami a tsakiyar birnin Moscow domin nunawa cewa akwai kumbiya-kumbiya a zaben shugaban kasar da aka yi.

Tun farko dai jami'an zabe a Rashar sun ce, yawan mutanen da suka fito domin jefa kuri'a ya ma wuce na zaben 'yan majalisar dokoki da aka yi a watan Disambar bara da kuma zaben shugaban kasa na shekara ta 2008.

Karin bayani