An samu kura-kurai a zaben Rasha-EU

putin
Image caption Vladmir Putin ya yi kokan murna

Masu sa-ido a zaben shugaban kasar Rasha, na kungiyar tsaro da hadin kan Turai - OSCE - sun ce, an sami kura-kurai a lokacin zaben na ranar Lahadi.

A cewarsu, kura-kuran sun hada da wadanda aka yi kafin gudanar da zaben.

Wani jami'in kungiyar ya ce "ko da yake dukan 'yan takara sun gudanar da kamfen dinsu ba tare da wani cikas ba, to amma a fili take cewa, an fitita dan takara guda a lokacin yakin neman zaben".

A cewar masu kula da zaben, an sami kura-kurai a lokacin kidayar kuri'u.

To amma kuma in ji su, ba tababa mista Putin ne yayi nasara da rinjaye sosai.

Wakiliyar BBC ta fuskar diplomasiyya ta ce "fadar gwamnatin Kremlin za ta dauki wannan a matsayin wani tabbaci na sakamakon karshe da hukuma ta bayar, inda ta ce Vladimir Putin ne ya lashe zaben da kusan kashi sittin da hudu cikin dari".

Karin bayani