'Yan gudun hijirar Homs sun ce dakarrun gwamnati sun ci zarafinsu

Garin Homs Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi raga-raga da sassan birnin

Mutanen dake tserewa daga birnin Homs na kasar Syria sun shaida wa BBC irin cin zarafin da suka ce dakarun gwamnati ke yi a wajen ciki har da kashe kananan yara.

Wasu Iayaye sun shaida wa wakilin BBC a Homs cewa an yanka dansu dan shekara goma sha biyu.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ayarin kayayyakin agaji na biyu ya isa Homs, amma an ajiye su a wajen unguwar Baba Amr wadda akai raga-raga da ita.

Mutanen da suke tserewa daka birnin Homs na kasar Syria sun bayar da cikakkun bayanai game da abinda suka ce halin rashin tausayi da azabtarwar da jami'an tsaro ke yi, wanda ya da kisan kananan yara.

Wasu iyalai sun shaida wa BBC cewa an yaka makogwaron dan su mai kimanin shekaru goma sha biyu wanda ke cikin mutane talatin da shidan da aka tsare da kuma hallaka a birnin Homs.

Mai magana da yawun Ofishin kwamishiniyar Hukumar Lura da kare hakkin biladama na Majalisar Dinkin Duniya, Rupert Colville, ya shaidawa BBC cewar hukumar na matukar damuwa game wanann rahoton wasu iyali da aka yanka dansu mai kimanin shekaru goma sha biyu

Yace lallai wannan rahoto mummuna ne, kuma abin takaicin ma kusan rahoto iri daya ne da wanda suka ji a ranar Alhamis din da ta gabata game da unguwar Bab Amr.

Ya ce abin bakin ciki ne irin wanan abu na faruwa.

Kungiyar bayar da Agaji ta Red Crescent dai ta ce akwai iyalai da dama da suka tsere zuwa yankunan da ke makwabtaka da birnin Homs masu fama da hare hare da yanzu haka ke bukatar taimakon gaggwa.

Karin bayani