An dora tubalin gina sabuwar kasuwar Maradi

Mahamadou Isoufou Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Nijer Mahamadou Isoufou

A jamhuriyar Nijer shugaban Kasar Alhaji Mahamadu Isoufou ya kadamar da aikin fara ginin kasuwar garin Maradi.

Kusan shekaru biyu kenan da jahar ta Maradi ta kwashe ba ta da wata babbar kasuwa dukkuwa da cewa nan ne cibiyar kasuwancin kasar ta Nijar.

Har ila yau Shugaba Mahamadu Isufu ya kadamar da aikin gina hanyar gidan Roumji Tsarnawa a ranar Litinnin.

An saran idan aka kamalla gina sabuwar kasuwar za ta bunkasa harkokin kasuwanci a Maradi da kuma wasu sassan kasar ta Nijer.