'Za a kashe Amurkawan da suka yi ta'addanci'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Eric Holder

Ministan harkokin shari'ar Amurka, Eric Holder, ya kare abin da ya kira damar da gwamnatin kasar ke da ita akan wasu batutuwa, kamar kashe 'yan kasar wadanda suka aikata ta'addanci.

Mista Holder, ya bayyana cewa daukar wannan mataki zai yi daidai, idan dan Amurkar ya kasance jagora a kungiyar Al Qaeda, wanda ke kokarin halaka 'yan Amurka kuma aka kasa kama shi.

Jawabin na sa ya biyo bayan suka ne game da kisan wani jagora a kungiyar Al Qaeda wanda haifaffen Amurka ne wato Anwar al-Awlaqi da Amurka ta yi a kasar Yemen a bara, ta hanyar amfani da makami mai linzami.

Karin bayani