An kashe mutane 16 a fada tsakanin Fulani

najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, hukumomi a jihar Benue da ke arewacin kasar sun tabbatar da mutuwar mutane 16, sakamakon wani harin da fulani makiyaya suka kai a karamar hukumar Gwer ta yamma.

Hukumomin dai sun ce maharan, wadanda ake zargin sun fito ne daga makwabciyar jihar Nasarawa, sun kai harin ne a ranar Lahadi.

Shugabannin fulani na jihar Nasarawa dai sun ce mutanensu ne ke da alhakin kai harin a matsayin ramuwar gayya, bayan da suka zargi 'yan kabilar Tivi da ke jihar Benue da kashe masu shanu a kwanakin baya.

Sai dai shugaban karamar hukumar ta Gwer ya musanta wannan zargin.