An kai hare-hare da dama a arewa maso gabacin Najeriya

Abubakar Shekau shugaban Boko Haram Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotannin da muke samu yanzu nan sun ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wata kasuwa da ke garin Giedam da ke arewacin jihar Yobe.

An kuma kai irin wannan hari a garin Banki dake kan iyakar kasar Kamaru da Jihar Borno, inda jama'ar yankin suka ce suna jin karar harbe-harbe.

Haka ma zance yake a garin Kunduga na jihar Borno, inda muka samu labarin cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a masaukin gwamnati da ke cikin garin.

Har wa yau mun samu labarin hare-haren 'yan bidinga a garin Ashaka da ke Jihar Gombe.

A daya bangaren, Kungiyar Kare Hakkin Biladama ta Human Rights Watch ta yi Allah wadai da abin da ta ce kaddamar da hare-hare da kona makarantun firamare da dama a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Ta ce tun a farkon wannan shekarar ‘yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna lid daawati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, sun kai hare-hare tare da lalata makarantu akalla goma sha biyu da ke tsakiyar birnin.

Lamarin da ya haramta wa dubun dubatar yara samun damar karatu.

Ko a daren jiya ma sai da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wata makarantar firamare da ke birnin.

Hakan kuma ya zo ne a daidai lokacin da wasu yan bindiga suka harbe shugaban Hukumar kwastan mai lura da shiyyoyin Borno da Yobe.

Sun harbe shi ne a gidansa da ke garin Potiskum.

Karin bayani