Mitt Romney ya yi zarra a zaben Super Tuesday

Hoton Mitt Romney Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mitt Romney na gaisawa da magoya baya.

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Mitt Romney ya samu wasu nasarori a zabukan fidda gwani na Super Tuesday da kankanuwar tazara a zaben Jihar Ohio mai mahimmanci gaske.

Kamar yadda aka yi tsammani, ya samu nasara a jihar sa ta haihuwa Massachusetts, da Idaho, Vermont da virginia.

Mr Romney ya kuma yi nasara a jihar Alska, wadda abokin hammayar sa Ron Paul ya yi zaton zai lashe.

Rick Santourum ya lashe jihohi uku, yayinda Newt Gingrich ya lashe zaben a jihar sa ta haihuwa.

Mr Romney a yanzu shi ne kan gaba da wakilai 415 da suka yi alkawarin mara masa baya a babban taron jam'iyyar Republican na kasa da zai zabi dan takara a watan Agusta mai zuwa.

Dan takara dai na bukatar wakilai 1,144 domin a tsayar da shi takara a jam'iyyar domin kalubalantar shugaba Barack Obama a zaben watan Nuwamba mai zuwa.

Sai dai zaben Super Tuesday bai tabbatar da cikakkiyar nasara ga Mr Romney ba, a don haka abokan hamayyar sa har yanzu suna da fatan doke shi.

Karin bayani