Ana zanga-zanga a Afrika ta Kudu

Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption shugaban kasar Afruka ta kudu, Jacob Zuma

Kungiyoyin kwadago a Afrika ta Kudu suna gudanar da jerin gwano da zanga-zanga domin nuna adawa da sabon harajin amfani da hanyoyi da aka sanya a wasu garuruwan kasar.

Babbar kungiyar kwadago ta COSATU da take da mambobi sama da miliyan biyu ne ta shirya zanga-zangar ta yau.

Kungiyar dai ta gayyaci jamiyyun adawa da kuma sauran jama'ar gari don su kasance a zanga-zangar da suka ce gagaruma ce da ba a yi irinta ba shekaru da dama da suka wuce.

Masu zanga zangar dai za su yi ne don nuna adawa da bullo da kofofin biyan kudaden hanya wato toll gates masu sarrafa kansu.

Kuma suna fatan cewa matakin zai sa gwamnati ta janye muradin nata.

Sabon tsarin dai zai sa masu babura su biya cent 28 da 30 duk kilomita daya, haka kuma masu motoci mara nauyi zasu biya cent 30 da 58.

'Yan Kungiyoyin kwadagon dai na ganin wannan babu adalci saboda masu babura tuni suna biyan kudin harajin mai wanda za'a iya amfani da shi a gyara hanyoyin alumma.

Karin bayani