Gwamnonin arewa sun yi taro a Kaduna

kano Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun yi taro a Kaduna, inda suka tattauna a kan matsalolin tsaron da suka addabi yankin.

Ana kuma sa ran za su duba al'amurran da suka shafi tattalin arzikin yankin wanda ke fama da kuncin talauci da kalubalen tsaro.

A kwanan nan dai an ji wasu gwamnonin yankin baya ga batun tsaro na korafi, bisa rabon arzikin kasar,inda suke cewa da sake.

Taron na yau dai zai kuma zabi sabon shugaban kungiyar gwamnonin na jihar arewa bayan gwamnan jihar Niger, Mu'azu Babangida Aliyu ya kammala wa'adin shugabancin kungiyar.