Afruka ta kudu ta nemi afuwa ga Najeriya

zuma Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma

Gwamnatin Afruka ta Kudu ta nemi afuwa ga Najeriya bisa tasa keyar wasu 'yan Najeriya matafiya su 125 da ta yi, wadanda take zargi da mallakar takardun jabu na allurar rigakafin ciwon shawara.

An hana 'yan Najeriyar ne shiga kasar ta Afruka ta Kudu a lokacin da jirgin da ya kai su kasar ya sauka a birnin Johannesburg a makon jiya.

A wani mataki da ake ganin na ramuwar gayya ne, ita ma Najeriyar ta hana wasu 'yan Afruka ta Kudun su sama da dari da talatin shiga kasar a lokacin da suka sauka a filin jirgin saman Lagos.

Shi ma kamfanin zurga-zurgar jiragen sama na Arik Air, ya dakatar da zurga-zurga na dan lokacin zuwa Afruka ta Kudun saboda wannan al'amari.