Matakin soji a Syria zai jawo matsala-Annan

kofi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kofi Annan da Banki Moon

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya, kuma wakilin kungiyar kasashen Larabawa a Syria, Kofi Annan, ya yi gargadin cewa duk wani katsalandan na soja a Syria, zai dagula al'amura a kasar ne kawai.

Ya ce yana fatan kasashen da ke maganar amfani da karfin soja a kan Syriar, ba da gaske suke ba.

Yayin da yake jawabi gabannin wata ziyara da zai kai kasar ta Syria, Mr Annan ya ce ta hanyar tattaunawar siyasa ce kawai za a iya warware rikicin kasar ta Syria.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da 'yan adawan kasar ta Syria, da su yi aiki tare domin cimma maslaha, wadda za ta yi la'akari da bukatun al'ummar kasar.

Karin bayani