Za a yafewa Girka bashin da ake bin ta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firayim Ministan Girka Lucas Papademos

Gwamnatin kasar Girka ta lallashi akasarin bangarorin da ke bin ta bashi domin su yafe mata bashi na fiye da euro biliyan 100.

Gwamnatin ta bayyana cewa fiye da kashi tamanin cikin dari na mutanen da ke rike da takardun lamunin kasar sun amince su yafe mata bashin da ta karba daga garesu.

Wannan mataki zai sanya Girka ta samu sararawa daga kangin bashin da take ciki, sannan za ta kaucewa tsiyacewa.

Kazalika za ta samu damar ci gaba da kasancewa cikin kungiyar kasashen da ke amfani da kudin bai-daya na euro.

Amma duk da haka, wannan shiri ba zai sauya matsalar da Girka ke fuskanta ta koma-bayan tattalin arziki ba.

Don haka idan har kasar ta ci gaba da fuskantar koma-bayan a fannin tattalin arzikinta, za ta tsunduma cikin kangin tattalin arzikin da ba a taba fuskanta ba tun bayan yakin duniya na biyu.

Karin bayani