Takaddama ta barke tsakanin Birtaniya da Italiya

Chris McManus Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Chris McManus

Shugaban kasar Italiya, Giorgio Napolitano ya soki lamirin Birtaniya kan yunkurin da ya ci tura na kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a Nijeriya, inda aka kashe wani injiniya dan Birtaniya, da abokin aikinsa dan kasar Italiya.

Ya ce , dabi'ar da gwamnatin Birtaniya ta nuna sam ba su da wata hujja, da zata sa su kasa sanar da Italiya, ko ko ta nemi shawararta, a game da matakin sojan da aka dauka, wanda ya haifar da wannan sakamako.

Wato lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Christopher McManus da Franco Lamolinara.

Tun da farko wani wakilin BBC a Nijeriya ya bada bayani kan sa'o'in da aka kwashe ana musayar wuta, ya kuma ce ya ga gawarwakin wasu 'yan Nijeriya biyu.

Wata majioyar gwamnatin Birtaniya ta ce wasu dakarun musaman na Birtaniya ne suka jagoranci kai samamen.

To yanzu haka dai jama'a daga sassan daban-daban na birnin Sakkwato na ci gaba da kwarara domin kashe kwarkwatar idonsu zuwa gidan da a kai garkuwa da turawan biyu.

Ba ruwan mu - Boko Haram

Kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ta ce ba ruwanta a garkuwar da aka yi da turawan biyu.

"Ba mu da hannu a kame mutanen da ya kai ga kashe su a yunkurin da aka yi na ceto su," in ji mai magana da yawun kungiyar Abul Qaqa a wata tattaunawar da ya yi da 'yan jarida ta wayar tarho.

"Ba mu taba yin garkuwa da mutane ba, kuma hakan ba ya cikin tsarinmu, kuma ba mu taba neman kudaden fansa ba." In ji shi.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne dai ya ce 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi garkuwa da turawan biyu.

Jama'a da dama a jihar ta Sakkwato ma sun nuna shakkunsu a kan cewa kungiyar Boko Haram ce ta kame turawan biyu.

Karin bayani