An kori ma'aikatan lafiya dubu 25 a Kenya

Image caption Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki

Gwamnatin Kenya ta ce ta kori ma'aikatan kiwon lafiya guda dubu 25 saboda yajin aikin da suka shiga.

Wani jami'in gwamnatin kasar ya ce wadanda aka sallama din sun hada da ma'aikatan jinya da masu aiki a dakunan gwaje-gwaje.

Ya kara da cewa kwanannan za a dauki sababbin ma'aikata wadanda za su maye gurbin wadanda aka kora.

Kungiyar ma'aikatan ta yi watsi da korar da aka yiwa ma'aikatan tana mai cewa wata dabara ce kawai ta karya lagonsu.

Ko da a makon jiya, ma'aikatan gidan rediwon kasar sun yi yajin aiki kuma an yi musu irin wannan barazanar inda daga bisani aka sasanta.

Karin bayani