Mayakan Al Shabab sun kashe sojojin Habasha da dama

Somalia
Bayanan hoto,

Mayakan Al Shabab sun hallaka sojojin Kasar Habasha

Kungiyar masu tsatstsauran ra'ayin Islama a Somalia, waso Al Shabab ta kaddamar da wani hari kan dakarun Kasar Habasha inda ta kashe da yawa daga cikin sojojinsu.

Kungiyar Al Shabab ta yi kwantan bauna a wani sansanin sojin dake kan hanyar da ta hada garin Baidoa da kan iyakar.

Anyi ta gumurzu har na tsawon sa'o'i hudu.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan ita ce gwabzawa mafi muni tun da dakarun Habasha suka shiga Kasar a watan Nuwambar bara.

Kungiyar Al Shabab ta ce ta kashe dakarun sojin Habasha su saba'in da uku, amma gwamnatin Somalia ta ce an kashe 'yan gwagwarmayar arba'in da biyar.