An kashe wani basarake a Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan bindiga

Wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani basaraken gargajiya ranar Juma'a da daddare a garin Gombe da ke arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce an kashe dagacin unguwar Kagarawal, Alhaji Bello Kagarawal, ne bayan an idar da Sallar Isha'i.

Bayanai dai sun ce kisan basaraken ya jefa yankin cikin rudani da zaman dar-dar.

Haka kuma wasu 'yan bindigar sun halaka wani babban jami'in 'yan sanda a jihar Adamawa mai makwabtaka da jihar ta Gombe.

Lamuran dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tabarberwar tsaro a Nijeriyar a baya-bayan nan.

Karin bayani