An kona wani mutum kurmus tare da matarsa a garin Ajalari

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harkar tsaro na cigaba da tabarbarewa a yankin arewacin Najeriya

Mazauna Unguwar Ajilari dake birnin Maidugurin jihar Borno sun bayyana cewa wasu mutane ne da ba a san ko su wane ne ba su ka shiga gidan mutumin mai suna Malam Tijjani, mai sana’ar gyaran wutar lantarki, suka kona shi da matarsa dauke da juna biyu kurmus, kana su ka yi gaba.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar ta Borno, Samuel Tihze ya shaida wa BBC cewar yana bukatar a ba shi lokaci kafin ya yi duk wani karin bayani.

A can garin Bulabulin Nigaura da ke karamar hukumar Konduga a kudancin jihar ta Borno kuwa, rahotanni na cewa wasu mahara ne suka dagargaza caji ofis na garin da bama-bamai a jiya, inda kuma yanzu haka bayanai ke cewa wasu mazauna garin sun tsere daga cikinsa domin fargabar abinda ka iya biyo bayan harin na bama-bamai.

Rundunar 'yansandan jihar ta Borno dai ta bayyana cewa jami’inta daya ya rasa ransa a harin.

Jihar ta Borno dai ta dade tana fuskantar hare-haren 'yan bindiga da kuma bama-bamai da kan yi sanadiyyar hasarar rayuka na jami’an tsaro da na farar hula, kuma kungiyar na ta Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda'awati wal jihad kan dauki alhakin kai wasu daga cikin jerin hare-haren, amma dai babu tabbaci ko ita keda alhakin harin na baya-bayannan.

Karin bayani