'Mutane miliyan daya da rabi na bukatar agaji a Syria'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Syria

Hukumomin bayar da agaji da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya sun ce kimanin mutane miliyan daya da rabi ne ke bukatar taimakon abinci da sauran kayan masarufi a kasar Syria.

Don haka ne hukumomin ke shirin yadda za su kai kayayyakin agaji cikin kasar.

Sai dai har yanzu suna jiran izini daga wajen gwamnatin kasar domin su shiga cikinta.

A farko wannan makon ne dai shugabar hukumar bayar da agaji da ke Majalisar Dinkin Duniya, Valerie Amos, ta je garin Homs na Syriar inda ta ce ana matukar bukatar agaji a kasar.

Annan zai je Syria

A ranar Asabar ne ake sa ran wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Larabawa, Kofi Annan, zai ziyarci Syria a wani yunkuri na kawo zaman lafiya a kasar.

A ziyarar, wacce zai kwashe sa'oi ashirin da hudu yana gudanarwa, Mista Annan ya ce yana sa ran cimma tsagaita bude wuta da kuma bude kofofin kai agaji ga kasar.

Ranar Juma'a shugaban kungiyar 'yan adawa mafi girma a Syria, Burhan Ghalioun, ya yi watsi da kiran da Mista Annan ya yi ga 'yan adawar kan su sasanta da gwamnatin shugaba Assad.

Ya ce kiran abin takaici ganin cewa Mista Assad na ci gaba da kashe al'ummar kasarsa.

Karin bayani