Sojan Amurka ya harbe 'yan Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Amurka a Afghanistan

Rundunar sojin kasashen waje da ke Afghanistan da hadin gwiwar hukumomin leken asiri na kasar sun ce suna gudanar da bincike bayan da wani sojin Amurka ya harbe 'yan Afghanistan guda uku babu- gaira-babu-dalili.

Sojin dai ya fice ne daga sansaninsu da ke lardin Kandahar da daddare kuma ba a san inda ya nufa ba.

A wata sanarwa da rundunar sojin kasashen waje da ke Afghanistan din ta fitar, ta bayyana takaicinta da aukuwar lamarin.

Ta mika ta'aziyyarta ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon iftila'in.

Kakakin gwamnan Kandahar ya ce lamarin ya auku ne a gundumar Panjwai .

Sasantawa da 'yan Taliban

Wannan lamarin ya auku ne a daidai lokacin da hukumomi a kasar ke cewa wadansu manyan 'yan kungiyar Taliban da Amurka ke tsare da su a gidan yarin Guantanamo Bay, sun amince a mayar da su gidan yarin da ke kasar Qatar.

Sai dai kisan da sojin Amurka ya yi wa 'yan Afghanistan din na iya yin kafar-ungulu a kokarin samun zaman lafiya a kasar.

Karin bayani