Tunawa da ranar da girgizar kasa ta aukawa Japan

Image caption Irin barnar da girgizar kasa ta yi a Japan

An dakatar da zirga-zirga a Japan bayan da jama'a suka yi tsit na wani dan lokaci don tunawa da zagayowar ranar da bala'in tsunami ya aukawa kasar a bara.

Tun a jiya ne aka fara addu'o'in tunawa da wadanda suka rasu a wasu sassan kasar.

Lamarin dai ya yi sanadiyar lalacewar tashoshin nukiliyar Fukushima da ke kasar.

Kimanin mutane dubu goma sha shida ne dai hukumomi a Japan suka tabbatar cewa sun rasa rayukansu sanadiyar bala'in.

Kazalika mutane fiye da dubu uku ne suka bace.

Karin bayani