Mun gaji da sojojin kasashen waje a Afghanistan

sojoji Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Amurka a Afghanistan

Majalisar dokokin Afghanistan ta amince da wani kudurin doka da aka tsara da kaukausar lafazi kan kisan wasu fararen hula 16 da wani sojin Amurka ya yi a kasar.

Kudurin ya ce jamaa sun gaji da hakuri da irin abubuwan da sojojin kawance ke yi a kasar ta Afghanistan.

Wakilin BBC ya ce majalisar dokokin Afghanistan din ta kuma ce wajibi ne a yiwa sojan na Amurka sharia a bainar jamaa a wata kotun Afghanistan.

Sai dai a karkashin 'yarjejeniyar tsaron dake tsakanin kasashen 2, rundinar sojin Amurka ce za ta yi ma shi sharia.

Tun farko shugaba Hamid Karzai ya tura wata tawagar manyan jami'ai zuwa lardin Kandahar, domin gudanar da bincike a kan kisan mutanen.

Sojan ya hallaka mutanen ne, wadanda suka hada da kananan yara 9, a cikin gidajensu a ranar Lahadi da asuba.

Tuni dai shugaba Obama ya nemi afuwa, tare da nuna takaicinsa da kisan.

A wanin labarin kuma ana nuna matukar damuwa cewa mai yiwa wasu munanan abubuwa na iya biyo bayan kisan fararen hular.

Wasu majiyoyi na kusa da shugaba Karzai, sun ce al'ammarin zai kara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da kasar ta Afghanistan.

Karin bayani