Bukatar ruwa ta karu a duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bukatar ruwa ta karu a duniya

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna cewa yawan bukatar ruwa ya karu sosai a duniya don haka dole ne a sauya tunani akan yadda za a wadata duniya da ruwa.

An fitar da rohoton ne a lokacin da ake fara wani babban taron duniya akan ruwa da ake yi a birnin Merseille na kasar Faransa.

Rohoton ya ce yayin da bukatar ruwa a duniya ke karuwa, yawan ruwan da ake samarwa kuwa sai raguwa yake yi saboda sauyin yanayi.

Olcay Unver shi ne ya rubuta rohoton, ya ce, ''Kira muke yi ga duk masu fada a ji da su yi la'akari da matsalar karancin ruwa a lokacin da suke yin tsare-tsaren su da kuma zayyana manufofin su''.

Karin bayani