Marubuta sun bukaci Jonathan ya yi murabus

jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Kungiyar marubuta masu rajin kare hakkin bil'adama a Najeriya,ta bukaci shugaba Goodluck Jonathan da ya sauke wajibin da ke wuyansa, na kare rayuka da dukiyar al'umar kasar, ko kuma ya yi murabus.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne, bayan harin bom din da aka kai a kusa da wata majami'a a Jos, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum goma, tare da jikkata wasu da dama.

Matsalar tsaro a Najeriya ta zama tamkar ruwan dare a kasar, inda ake kara samun zaman zullumi tsakanin 'yan kasar.

A 'yan watannin na 'yan kungiyar Boko Haram sun yita kaddamarda hare-hare a sassa daban daban na kasar.

Karin bayani