David Cameron zai kai ziyara white House

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fira Ministan Burtaniya, David Cameron, yana yiwa yan Jaridu jawabi

Fira Ministan Burtaniya, David Cameron zai kai ziyara fadar white house domin ganawa da takwaransa na Amurka, Shugaba Barack Obama.

Ana saran dai Shugabannin biyu zasu tattauna akan amincewa da shirye- shiryen kawo karshen ayyukan dakarun Amurkar dana Burtaniya a Kasar Afghanistan zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.

Sai dai ganawar shugabannin biyu na zuwa ne a lokacin da 'yan kasar afghanistan din ke cike da fushin kisan wasu fararen hula su goma sha shida da wani soja bamaurke ya yi.

Haka kuma ana saran zasu tattauna akan batun kire makamin nukiliya da Kasar Iran keyi.

Karin bayani