Isra'ila da Falasdinawa sun ajiye makamai

Hakkin mallakar hoto r
Image caption shugabannin hamas

Rahotanni daga Gabas ta Tsakiya na cewa an samu yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da kuma Falasdinawa, bayan da aka shafe kwanaki hudu ana artabu.

Akalla Falasdinawa ashirin da biyar ne suka rasu a sanadiyyar hare-haren da Isra'ilan ta kai ta sama a yankin Gaza tun ranar Juma'ar da ta gabata.

Ya zuwa yanzu dai babu wadansu bayanai da suka fito a hukumance daga bangarorin biyu, amma rahotanni sun nuna cewa kasar Masar ce ta shiga tsakani.

Tun farko dai Isra'ila na cewa ba zata tsagaita wuta ba har sai kungiyar Hamas ta dakatar da kai mata hare-haren rokoki.

Akalla dai Hamas ta harba rokoki sama da dari biyu, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama wadansu kuma suka jikkata.

Kafin yarjejeniyar dai, Hamas ta ce ba za ta fara tsagaita wuta ba saboda Isra'ila ce ta fara kai hare-haren ranar Juma'ar da ta gabata.

Samar da yarjejeniyar zaman lafiyar dai zai iya rage yawan zubar da jini da fargaba ga al'ummar bangarorin biyu.

Karin bayani