An kaiwa wata tawagar gwamnati hari a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojan Amurka

Masu tada kayar baya a Afghanistan sun bude wuta a kan wata tawagar gwamnati da ta kai ziyara zuwa daya daga cikin kauyukan da ake zargin sojan Amurka ya kashe farar hula goma sha shidda a ranar lahadi data wuce.

Sai dai dakarun Afghanistan su ma sun mayar da martani a lokacin da aka kaiwa tawagar hari a kauyen Balandi a lardin Kandahar inda Soja daya ya halaka kuma tuni tawagar ta koma birnin Kandahar .

Bakin da suka hada da 'yan uwan shugaba Karzai su biyu sunyi magana da iyalan da harin ranar juma'a ya shafa.

Daga farko a birnin Jalalabad daruruwan dalibai sunyi wata zanga zanga akan tituna game da kisan da sojan Amurkan yayi.

Daliban sun rika shewa suna kiran mutuwa ga Amurka kuma sun bukaci a yiwa soja sharia a gaban bainar jama'a