Obama ya soki China akan boye ma'adinai

obama
Image caption Barack Obama na Amurka

Shugaba Obama na Amurka ya ce zai kai China kara a kungiyar kasuwanci ta duniya game da dauninta na fitar da ma'adinan da ba kasafai ake samunsu ba ta yadda Amurka za ta samu adalcin cinikayya a tattalin arzikin duniya.

Mista Obama ya ce masu yin kayayyaki a Amurka na bukatar ma'adinan domin kera kayayyakin zamani kama daga motoci masu amfani da makamashi fiye da daya zuwa wayoyin salula -- to amma China na yin katsalandan a kasuwar domin takaita samar da su.

Ya ce "don haka gwamnatinmu za ta shigar da wannan kara a yau, kuma za ta ci gaba da aiki a kowace rana don baiwa Amurkawa ma'aikata da kuma Amurkawa yan kasuwa adalci a tattalin arzikin duniya".

Kungiyar Tarayyar Turai da Japan ma sun shigar da koke game da batun.

Karin bayani