Praministan China ya nemi a yi sauyin siyasa

wen jiabao Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Praminista Wen Jiabao

Praministan China, Wen Jiabao, ya yi kwakkwaran gargadi a kan bukatar kara samun sauyin siyasa -- yana mai cewar idan ba a yi hakan ba, makomar China na cikin hadari.

Mr Wen ya ce tsarin shugabanci na jam'iyya, da kuma kasar na bukatar sauyi, ko kuma za a iya yin asarar ci gaban tattalin arzikin da aka samu, kuma China za ta iya fuskantar rikicin siyasa kamar wanda aka samu a lokacin juyin juya hali ta fuskar dabi'a da al'adu.

Mr Wen na magana ne a karshen zaman majalisar dokokin China na shekara shekara - zaman da shi ne nasa na karshe kafin mika mulki da ake yi sau guda cikin kowane shekaru goma.

Karin bayani