'Yan-sanda na binciken faduwar helikwabtansu

Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Mohammed Abubakar shugaban 'yansandan Nigeria

Rundunar 'yan sandan Najeriya tace, cewa za'a gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa faduwar wani jirgi mai saukar-ungulu, wanda yayi sanadin mutuwar mataimakin babban sepeta-janar da ke kula da sashen ayuka na rundunar da wasu jami'ai.

Jirgin ya fadi ne a kan wasu gidaje dake kusa da wata kasuwa a kan hanyar Rukuba dake garin Jos, kuma wasu daga cikin farar hula dake wajen su ma sun rasa rayukansu.

Bayanai dai na cewa jirgin saman ya fadi ne da misalin karfe goma sha biyu na ranar yau a bayan kasuwar hanyar rukuba inda kuma ya fadi a kan wasu gidaje na farar hula.

Jirgin dai na rundunar tsaro ta musamman mai aikin samar da zaman lafiya a jihar ta Filato ne mai dauke da manyan jami’an yan sanda.

Kakakin rundunar yansandan jihar Filato ASP Samuel Dabai, ya shdewa BBC cewa dukkan manyan jami’an yan sanda dake cikin jirgin sun rasa rayukansu ciki kuwa har da mataimakin babban sifeton yan sandan Nijeriya mai kula da aikace-aikace, DIG John Haruna da kuma wasu manyan jami’an yan sanda uku.

Kakakin rundunar yansandan yace kawo yanzu suna ci gaba da tattara bayanai game farar hula dasuka rasa rayukansu.

Sai dai wata majiya ta shedawa BBC cewa an gano gawawwakin farar hula biyar, da kuma kai wata mata asibiti a sakamakon faduwar jirgin a kan gidajen da suke zama.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin hadarin jirgin ba mai saukar ungulu na jami’an tsaro ba, amma dai mazauna yankin na jirgin ya fadi, sun bada labarin cewa kafin rikitowar jirgin kasa, ya yo kasa-kasa sosai, kana sun ga wani irin hayaki na fita daga jirgin.

Jirgin mai saukar ungulu dai, dama yana sintiri ne a sararin samaniyar birnin na Jos mai yawan fama da rikice-rikice masu nadaba da kabilanci da addini da kuma siyasa sa’adda da ya rikito a waje-jen kasuwar ta hanyar rukuba.