Muna samun nasara a Afghanista-Obama

obama cameron Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Obama da David Cameron

Shugaba Obama da kuma Pirayim Ministan Birtaniya, David Cameron dake ziyara, duk sun bayyana aikin kasashen Duniya a Afghanistan da cewar yana samun ci gaba na zahiri.

Mista Obama ya ce Amurka da Birtaniya sun kudurci aiwatar da shirinsu na mayar da cikakken alhakin tsaro ga dakarun Afghanistan a cikin shekaru biyu.

Ya ce"abun da ba za a iya musantawa ba, kuma abunda ba zamu taba mantawa ba shi ne cewar dakarunmu na samun ci gaba na zahiri ainun., ta hanyar kawar da al-Qa'ida, da takura faffakar Taliban da kuma horadda dakarun Afghanistan ta yadda za su iya yin jagoranci , sannan dakarunmu su dawo gida".

A kan Iran , ya ce dukanin kasashen sun yi amannar har yanzu akwai lokaci na bin kokarin diplomasiya don hana kasar samun makamin Nukiliya.

Mista Obama ya sake jaddada goyon bayan dukanin kasashe na samun mulkin demokuradiya a yankin gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika.

Karin bayani